14 Maris 2020 - 05:20
Najeriya : An Bai Wa Tsohon Sarkin Kano ‘Yanci

Rahotanni daga Najeriya na cewa an bai wa tsohon sarkin Kano, ‘yanci inda yanzu haka ya yanke shawarar zuwa jihar Lagos.

(ABNA24.com) Rahotanni daga Najeriya na cewa an bai wa tsohon sarkin Kano, ‘yanci inda yanzu haka ya yanke shawarar zuwa jihar Lagos.

Tunda farko dama wata kotu a Abuja ta umarci a bai wa tsahon Sarkin damar shiga ko ina a fadin kasar ta Najeriya ban da jihar Kano.

A ranar Litinin ne gwamnatin jihar Kano ta tsige Sarki Sanusi na II daga kan sarauta bayan ta zarge shi da rashin biyayya da kin mutunta gwamnatin jihar, da wulakanta al’adun al’umma da kuma masarautar da yake jagoranta, zargin da a cen baya ya sha musantawa.

A ranar ne kuma aka dauki tsohon sarkin zuwa garin Loko da ke jihar Nasarawa, amma washe gari an mayar da shi garin Awe.



/129